ABNA24 : Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen Iran ɗin ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da yayi da tashar talabijin ɗin Press TV da ke watsa shirye-shiryenta daga nan Tehran inda ya ce: Kamar yadda aka sha faɗi ba za a taɓa amincewa da tsarin cire takunkumi a mataki-mataki ba.
Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya ƙara da cewa, wajibi ne kuma wannan magana ta cire takunkumi ta zamanto a fili sannan kuma Iran ɗin ta tabbatar da hakan a ƙas ba wai kawai a magana ba.
Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen na Iran yana mayar da martani ne ga mataimakiyar kakakin Ma’aikatar wajen Amurka Jalina Porter na wani shiri da ake gani na tattaunawa tsakanin wakilan Iran da na sauran ƙasashen da suke cikin yarjejeniyar nukiliyan kan yarjejeniyar da yadda za a sake rayar da ita.
342/